5 Satumba 2024 - 14:20
Shugaban Kungiyar Ansarullah Ta Yaman: Laifukan Dabbanci Na Isra'ila Ya Kai Ga Cutar Da Zukatan Wadanda Ba Musulmi Ba.

Musulman Gaza na fama da munanan hare-hare da kashe-kashen gilla da Isra'ila ke yi, wanda ke cutar da al'ummomin kasashen da ba musulmi ba.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul-Baiti As - ABNA - ya kawo maku rahoto bisa nakaltowa daga shafin sadarwa na IRNA cewa Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yaman ya fara jawabinsa a yau a daidai lokacin da watan Rabi'ul Awwal ya shiga, inda ya yi bayani kan abubuwan da ke faruwa a yankin ciki har da Gaza.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa, a a yau ranar Alhamis shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdul Malik al-Houthi, a farkon jawabin nasa, ya taya daukacin al'ummar musulmin duniya murnar shigowar watan Rabi'ul Awwal mai alfarma. A kowace shekara al'ummar kasar Yemen na bayar da kulawa ta musamman ga maulidin manzon Allah (S.A.W), kuma a wannan lokaci tana da ayyuka masu fa'ida da dama wadanda suka kunshi na ilimi da jihadi na tsawon makonni.

Sayyid Al-Houthi ya fayyace cewa: "Ya kamata a ba da kulawa ta musamman ga Jihadi da kafirai da munafukai a dukkan bukukuwa da ayyukan maulidin Annabi Muhammad (SAW) a yanayin hare-haren da Amurka da Isra'ila suke kai wa al'ummar Musulmi.

Shugaban na kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa yana da hadari a bar Jihadi a tafarkin Allah a yayin hare-hare da kuma laifuffukan da makiya suka dora kan al'ummar musulmi.

Ya ci gaba da yin tsokaci kan abubuwan da ke faruwa a Gaza inda ya ce: Musulman Gaza na fama da munanan hare-hare da kashe-kashen gilla da Isra'ila ke yi, wanda ke cutar da al'ummomin kasashen da ba musulmi ba.

Ana cikin kammala...